IQNA

Taro Mai Taken Kyawawan Dabi’u A Mahangar Musulunci Da Kiristanci A Ethiopia

23:10 - October 03, 2019
Lambar Labari: 3484115
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taron kara wa juna sani kan kyawawan dabi’u a mahangar muslunci da kiristanci a Habasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an yi wata ganawa a birnin Addis Ababa tsakanin shugaban cibiyar buknasa al’adun muslunci Salman Rostami, da kuma Yakub Kidibo shugaban jami’ar nazarin addinai ta Habasha.

A yayin ganawar bangarorin biyu sun cimma matsaya kan gudanar da wani taron karawa juna sani kan kyawawan dabiu a mahangar addinain kiristanci da musulunci, wanda zai gudana a babban dakin taruka na jami’ar nazarin addinai a birnin Addis Ababa.

Nan da makonni uku masu zwa ne dai ae sa ran za a gudanar da taron, wanda zai samu halartar masana daga ciki da wajen kasar, daga bangarorin musulmi da kuma mabiya addinin kirista, domin kara karfafa dankon alaka da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan biyu.

3846738

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، karfafa ، Habasha ، Ethiopia
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha