IQNA

23:50 - October 06, 2019
Lambar Labari: 3484124
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da tarukan ranar Imam Hussain (AS) a birnin San Francisco na jihar California a Amurka.

Kamfanin dillancin lbaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a ranar 12 ga wannan wata na Oktoba, za a gudanar da tarukan ranar Imam Hussain (AS) a birnin San Francisco na jihar California a Amurka daga karfe 10 zuwa 15.

Za a gudanar da jerin gwano, sannana gabatar da jawabai, kuma za a yi sallar jam’I kamar yadda kuma za a raba abinci ga mabukata a cikin birnin.

Cibiyoyin mabiya mazhabar ahlul (AS) ne na birnin za su dauki nauyin taron, da suka hada da cibiyar Muhammadiyya, Fatimiyyah, Quba, masallacin Imam Hussain (AS) masallacin Fatima (AS) da masallacin manzo (SAW).

 

 

3847634

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: