IQNA

22:22 - October 12, 2019
Lambar Labari: 3484146
Bangaren kasa da kasa, za a bude wani dakin ajiye kayan tarihin manzon Allah da addinin mulsunci a kasar Indonesia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayan kasar Saudiyya, kasar Indonesia za ta zama kasa ta biyu a duniya da za ta bude  dakin ajiye kayan tarihin manzon Allah da addinin mulsunci a kasar.

Bayanin ya ce za a bude wannan dakin kayan tarihi nea  garin Depok da ke cikin gundumar Jawa ta yamma, a kusa da babbar jami’ar musulunci da ke yankin.

An sanya hannu kan gina wanann wuri tsakanin kungiyar limaman musulmi na kasar Indonesia, da kuma cibiyar malamai ta duniya a  abban ginin kungiyar kasashen musulmi da ke birnin Jidda.

Abin tuni dai shi ne, dakin ajiye kayan tarihin manzon Allah guda daya ne ke akwai a birnin Madina Almunawwara.

 

3849252

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: