IQNA

21:50 - October 18, 2019
Lambar Labari: 3484166
Bangaren kasa da kasa, wata musulma ta kai kara kan take hakkinta na addini a jihar Delaware a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin USA Today ya bayar da rahoton cewa, Madina Brown wata musulma ce wadda ta kai kara a kotu kan take hakkinta na addini a jihar Delaware da ke kasar Amurka.

Bayanin ya ce wannan musulma ta nemi aiki a gidan kason jihar a cikin 2011, amma saboda lokacin da ta je wurin ta saka lullubi, sai  aka ki daukarta, amma shekara daya bayan haka ta sake komawa amma ba tare da lullubi ba, sai aka dauke ta.

A cikin shekara ta 2014 ta yanke shawara cewa zata yi lullubi domin bin umarnin addininta, daga lokacin kuma sai mahukuntan gidan kason suka kore ta daga aiki.

Bayan kwashe shekaru biyar ba tare da an nema ta ba, ta yanke shawarar shigar da kara a kotu domin bi mata hakkinta, yayin da babban kwamitin musulmin kasar Amurka ya nuna cikakken goyon bayansa gare ta, tare da daukar mata lauyoyi.

3850771

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: