IQNA

Taron Kara wa Juna Sani kan Kur’ani A Wata Jami’ar Kasar Jamus

22:57 - October 23, 2019
Lambar Labari: 3484183
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron karawa juna sani kan kur’ani mai tsarki a jami’an Monster da ke kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,a  cikinmakonni biyu masu zuwa ne za a gudanar da taron karawa juna sani kan kur’ani mai tsarki a jami’an Monster da ke kasar Jamus wanda Muhannid Khu Khorshid shugaban bangaren koyar da ilmomin sanin ubangiji na jami’ar zai jagoranta.

Bayanin ya ce wannan taro zai samu halartar masana daga kasashen duniya daban-daban, inda za su gabatar da makalolinsu kan nazarin da suka yi dangane da kur’ani da kuma addinin muslunci.

Daga jami’ar Kintani ta Amurka wasu masana zasu halarta, kamar yadda Joseph Lombard daga jami’ar Hamad Bin Khalifa da ke Qatar shi ma zai halarta, haka nan za a gabatar da makaloli da masana daga jami’oin Irna suka rubuta kan wannan fanni.

 

3851910

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha