IQNA

Rauhani: Babu Inda Amurka Ta Yi Nasara A Gabas Ta Tsakiya

23:43 - October 26, 2019
Lambar Labari: 3484191
Shugaba Rauhani ya bayyana irin tsayin dakan da kasashen Iran da Venezeula suke yi a gaban Amurka da cewa abin koyi ne

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a jiyaa lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Venezeula Nicolas Maduro, a gefen taron shugabanin kasashe mamobi a kungiyar ‘yan ba ruwanmu.

Rauhani ya ce; akwai kyakkyawar alaka mai karfi tsakanin kasashen Iran da Venezeula, wadda ta ginu a kan girmama juna da kuma yin aiki tare a dukkanin bangarori, kamar yadda kasashen biyu suke da mahanga guda ta yin tsayin daka domin su rayu a cikin ‘yanci, da kuma kin mika kai ga manufofin ‘yan mulkin mallaka.

Ya kara da cewa Iran za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada tare da kasar Venezeula a dukkanin bangarori na tattalin arziki, cinikkaya, noma, ilimin kimiyya da sauransu.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Venezeula Nicolas Maduro ya jinjina wa kasar Iran dangane da yadda ta kasance tare da Venezeulaacikin dukkanin yanayin da ta samu kanta, na matsin lamba daga Amurka da kawayenta, inda ya ce tsayin daka a kan siyasar cin gishin kai da ‘yanci ita kadai ce mafita ga Venezeula da Iran da sauran kasashe masu ‘yancin siyasa.

 

3852336

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rauhani ، Iran ، venezuela ، Maduro
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha