IQNA

23:46 - October 26, 2019
Lambar Labari: 3484192
Bangaren kasa da kasa, an saka wani dadadden kwafin kur’ani a gidan ciniki na Sotheby’s da ke Landan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sothebys wani gidan sayar da kayan tarihi ne da aka kafa a birnin Landan a ranar 11 ga watan Maris 1744, inda masu kudi daga birane irin su Paris, New York, da kasashen India Hong Kong da saurasu suke zuwa, domin sayen dadaddun abubuwa na tarihi da kudade masu tsada.

An saka ma wannan wuri sunan mutumin da ya fara assasa shi, inda kuma har yanzu wannan harka take gudana a tsawon shekaru kusan dari uku.

A ranar 23 ga wanann wata na Oktoba ma an nuna wasu kayan tarihin mslunci a wannan wuri da nufin sayar da su, daga ciki har da wani dadadden kwafin kur’ani mai tsarki, wanda aka rubuta shit un karni na 16 miladiyya, kimanin shekaru dari biyar da suka gabata.

 

3849963

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Landan ، Amurka ، sayarwa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: