Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman taron ne a cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin, inda Hojjatol Islam Mahmud Muntezari ya gabatar da jawabi.
A cikin jawabin nasa ya bayyana matsayin manzon Allah (ASW) da cewa shi ne abin koyi ga kowa a duniya, bag a muuslmi kawai ba, har da sauran dukkanin ‘yan adam, kuma hakan bai takaitu da lokacinsa, dabiunsa abin koyi ne tun daga lokacin rayuwarsa har zuwa ranar tashin kiyama.
Ya ce shi ne mutum da ya kawo sauyi a cikin lokacin jahiliyya da kyawawan dabiunsa, kamar yadda yada kuma halayensa suke abin koyi tun daga rayuwarsa ta kuruciya, kamar yadda hakan ya tabbtabbataata a tarihi.