IQNA

23:33 - October 30, 2019
Lambar Labari: 3484207
Bangaren kasa da kasa, wata musulma mai sanye da lullubi ta zo ta daya a gasar tseren dawaki a kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Evening Standard cewa, a karon farko wata musulma mai sanye da lullubi ta zo ta daya a gasar tseren dawaki a kasar Birtaniya.

Wannan musulma mai suna Khadijah Mellah ta bayyana cewa, ta shiga wannan gasa ne wadda ake gudanarwa domin ayyukan alhairi ta Goodwood, da nufin karfafa gwiwar musulmi wajen shiga cikin abubuwan da ake yi.

A daren jiya an nuna wani fim a birnin Brixton na kasar Birtaniya dangane da wannan mata, da kuma rayuwarta da yadda ta shiga wannan gasa.

Mellah dalibar jami’ar Brixton ce wadda take karatun injiniya, ta bayyana cewa ta yi farin cki matuka dangane da nasarar da ta samu a wanann gasa, kuma ta tabbatar wa sauran mata musulmi cewa za su iya.

3853313

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: