IQNA

21:38 - November 02, 2019
Lambar Labari: 3484215
Jam'iyyar gurguzu a Sudan ta zargi gwamnatocin Saudiyya da UAE da yunkurin karkatar da juyin da aka yi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto cewa, kamfanin dilalncin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Mukhtar Alkhatib babban sakataren jam'iyyar gurguzu a kasar Sudan, kuma babban mamba na kawance 'yanci da canji a kasar da suka kawo karshen mulkin Albashir, ya zargi gwamnatocin kasar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa wajen yunkurin rusa juyin da al'ummar kasar suka yi.

Ya ce gwamnatocin wadannan kasashe sun yi ta tuntubar wasu daga cikin jam'iyyun siyasar kasar da nufin yin amfani da wasu wajen karkata akalar zanga-zangar da al'ummar kasar suka gudanar, wadda ta kawo karshen mulkin kama karya, amma ba su samu nasara ba, amma har yanzu suna bin mahukuntan kasar a bayan fage.

Haka nan kuma babban sakataren jam'iyyar 'yan gurguzu ta kasar Sudan ya yi kira da Sudan ta kawo karshen shiga cikin kawancen masu yaki da al'ummar kasar Yemen, domin ci gaba da hakan na matsayin cin amanar kasa.

3853995

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، matsayin ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: