IQNA

23:54 - November 03, 2019
Lambar Labari: 3484218
Bangaren kasa da kasa, kwamitin zakka a Najeriya yana samar da hanyoyi na ayyukan yi tsakanin matasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kwamitin zakka a najeriya ya raba kudi ad suka kai naiara miliyan 320 ga matasa a cikin jihohi 21 na kasar, inda matasa 2447 suka samu wannan tallafi.

Wannan dais hi ne karon farko da aka taba bayar da irin wadannan kudade ga matasa domin tallafa musu daga asusun zakka a kasar domin sama musu ayyukan yi.

Wannan kwamiti dai mai zaman kansa ne da baya da wata alaka da gwamnati, kuma yana gudanar da ayyukansa a mafi yawan lokuta  bangaren ayyukan jin kai da kuma tallafawa marassa galihu.

Wasu bangarori masu zaman kansu da suka hada da wasyu masu kudi suna goyon bayan wanann shiri.

 

 

3854162

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، goyon baya ، matasa ، hanyoyi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: