IQNA

23:50 - November 08, 2019
Lambar Labari: 3484235
Bangaren kasa da kasa,a yau an kammala gasar kur'ani ta duniya ta mata a hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, an kammala gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Dubai, wadda aka gudanara  karo na hudu mai taken Shaikha Fatima Bint Mubarak.

Wannan gasa dai ta kebanci mata ne zalla daga kasashen duniya daban-daban, inda aka kwashe tsawon kwanaki satin ana gudanar da ita.

Gasar ta samu halartar jami’an gwamnati da malaman addini gami da wakilan cibiyoyin addini na kasar, kamar yadda kuma aranar ta jiya wato ranar karshe, wadanda suka kara da juna su ne, Raudha Bint Abdulrazaq daga Malaysia, Fatima Rashed Salem Alsuwaidi daga Emarates, Ru’a Mahdi daka Kuwait, Hauwa Muhamam daga Kamaru, Husaina Jallo daga Saliyo.

Za a sanar da sunayen wadanda suka nuna kwazo domin basu kyautuka.

Zainab Faidhi ita ce ta wakilci Iran a wanann gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa.

 

3855401

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: