IQNA

18:28 - November 26, 2019
Lambar Labari: 3484275
Kungiyar kasashen larabawa ta gudanar zaman gaggawa kan batun gina matsagunnan yahudawa a Palastinu.

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi watsi da sanarwan da gwamnatin Amurka ta bayar na sake amincewa da gine-ginen da yahudawan Isra'ila suke yi a yankunan Palasdinawa da suka mamaye.

Babban sakataren kungiyar Ahmed Aboul Gheit ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a zaman da kungiyar ta gudanar.

Ya kuma kara da cewa matakin da Amurka ta dauka zai dawo da hannun agogo baya a kokarin sulhuntawa da ake yi tsakanin Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniyya.

A ranar 18 ga watan Nuwamban da muke ciki ne sakaren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan cewa Amurka ta dawo daga rakiyar doka wacce gwamnatin shugaba Jimmy Carter ta amince da ita a shekara 1978 na rashin amincewa da gine-ginen da yahudawa Isra’ila suke yi a yankunan Palasdinawa da ta mamaye.

A halin yanzu ta amince da dukkan gine-ginen da yahudawan suka yi a wadannan yankuna.

 

 

3859561

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: