IQNA

21:40 - November 27, 2019
Lambar Labari: 3484276
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana shirin fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Qatar da aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Bayanin ya ce dukkanin mahalrta wannan gasa dai daliban makamarantu ne, kamar yadda kuma adadin wadanda za su kara da juna a gasar zai kai dalibai 290.

Babbar manufar gasr dai ita ce karfafa gwiwar matasa masu sha’awar shiga harkokin kur’ania  kasar domin su ci gaba da kara bayar da himma.

Za a gudanar da gasar a  bangaren harda da zai hada da izihi na 10, sai kuma izihi na 15, da kuma na 20 zuwa na 25, daga karshe kuma za a karrama dukkanin wadanda suka nuna kwazo a gasar.

3860104

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Qatar ، kwazo ، gasar kur’ani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: