Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, dubban mutane ne suka gudanar da gangami a birane na kasar Birtaniya kan adawa da nuna wariya ga musulmi da ake yi a kasar.
Wannan gangami da jerin gwano na zuwa ne dai a daidai okacin da sakamakon jin ra’ayin jama’a ke nuni da cewa nuna kiyayya ga musulmi a kasar yana karuwa cikin sauri.
Mata musulmi da suke saka lullui dais u ne suka fi fuskatar matsaoli a wasu yankuan na kasar, inda har sukan fuskaci matsal wuraren ayyukansu da kuma makarantu.
Kasar Birtaniya na daya daga cikin kasashen turai da adadin musulmi yake ci gaba da karuwa a cikin sauri, lamarin da masu kiyayya da musulmi kasar suke kallonsa a matsayin wani babban hadari ga maomar kasar.