IQNA

9:14 - December 04, 2019
Lambar Labari: 3484290
Harkar musulunci ta fitar da wani bayani dangane da cikar shekaru hudu da kama sheikh Zakzaky Da Mai dakinsa.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a cikin wani bayani da harkar musulunci ta fitar, ta bayyana wannan lokaci da cewa shi ne na cikar shekaru hudu da kame Sheikh Zakzaky.

Bayanin wanda shugaban dandalin watsa labarai na harkar musulunci Ibrahim Musa ya sanya wa hannu ya yi ishara da cewa, tsare malamin da ake yi ba ya kan doka.

Inda bayanin ya ce tun kafin wannan lokacin kotun tarayya ta bukaci a saki malamin da ma dakinsa har ma da biyansu diyya, amma har yanzu ba a aiwatar da wannan umarni na kotu ba.

Baya ga haka kuma wani bangaren bayanin ya yi ishara da wajabcin mutunta hakkin dan adam, wanda ci gaba da tsare malamin da mai dakinsa da ma wasu magoya bayan harka ya yi hannun riga da hakana  cewar bayanin.

Tun a cikin watan Dismban 2015 ne dai jami’an sojojin Najeriya suka kaddamar da farmakia  kan gidan shekh Zakzaky, inda ska kashe daruruwan magoya bayansa, tare da kama shi bayan harbinsa da harsasan bindiga.

 

3861235

Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، Sheikh Zakzaky
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: