IQNA

23:33 - December 07, 2019
Lambar Labari: 3484299
Qais Khazali shugaban dakarun Asa’ib Ahlul Haq ya yi gargadi kan bullar fitina ta cikin gida a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Qais Khazali shugaban dakarun Asa’ib Ahlul Haq daya daga cikin bangarorin Hashd Sha’abi ya yi gargadi kan bayyanar makamai a kan tituna a cikin biranan Iraki.

Ya ce ya zama wajibi kan al’ummar Iraki su zama cikin fadaka kan makircin da ake kulla musu, na haifar da yakin cikin gida a kasar da nufin rusa ta.

Qais Khazali ya ce suna yin biyayya ga kiran da babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani ya yi, kan cewa makaman jami’an tsaro ne kawai ya kamata a gani kan tituna a biranan kasar Iraki.

3862177

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، lumana ، gargadi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: