IQNA

22:42 - December 08, 2019
Lambar Labari: 3484303
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce akwai tuntubar juna tsakaninsu da gwamnatin Najeriya kan batun sheikh Zakzaky.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce akwai tuntubar juna tsakaninsu da gwamnatin Najeriya kan batun sheikh Zakzaky domin ganin an kawo karshen tsare shi.

Ya ce ganin cewa kasashen Iran da Najeriya suna kyakkyawar alaka ta diflomasiyya, kuma akwai ayyuka da dama da suke hada kasashen biyu a matsayi na kasa.

A kan haka ya kara da cewa, dukkanin kasashen biyu suna da fahimtar juna a kan lamurra da suka hada su, kuma batun sheikh Zakzaky na daga cikin abubuwa da Iran Iran take tattaunawa da gwamnatin Najeriya a kansa, kuma akwai fatan ganin cewa an warware lamarin.

3862555

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: