IQNA

19:10 - December 15, 2019
Lambar Labari: 3484320
Ata’ullah Hana babban malamin mabiya addinin kirista a Quds ya caccaki Isra’ila kan hana kiristoci ziyarar birnin Qods.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Ata’ullah Hana babban malamin mabiya addinin kirista a Quds ya caccaki gwamnatin yahudawa kan hana kiristocin falastinu ziyarar birnin Qods a lokacin bukukuwan kirsimati.

Ya ce wannan mataki na nuna wariya ne da zalunci da take hakkin addini, domin kuwa babu wani dalili da zai sanya gamnatin yahudawan Isra’ila ta hana kiristoci gudanar da ayyukans an ibada.

Ya kara da cewa, wadannan taruka ne da ae gudanarwa tun shekaru fiye da dubu daya da dari takwas, kuma ba  ataba fasa gudanar da su, akan haka a halin yanzu yahudawa ba su da hurumin hana tarukan kirsimati a Quds.

A nasa bangaren kwaitin kiristoci da musulmi na Quds ya yi Allawadai da kakausar murya kan wannan mataki, wanda yakea  matsayi karya kudirin majalisar dinkin duniya na 1948.

An fara aiki da wannan kudiri  1949 wanda ya halastawa dukkanin falastinawa musulmi da kiristoci gudanarwa ayyukansu na ibada a birnin Quds ba tare da wani kangi ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3864111

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، Quds ، falastinawa ، kiristoci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: