IQNA

19:40 - December 17, 2019
Lambar Labari: 3484327
Babban malamin mabiya addinin kirista a Brazil bai amince da mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa Qyds ba.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Don Aurani Tampista babbar Cardinal na kasar Brazil, ya bayyana cewa dan shugaban kasar Brazil ya bayyana ra’ayinsa ne dangane da batun nuna goyon baya ga Isra’ila da uma batun dauke ofishin jakadancin Brazil zuwa Quds.

Babban malamin kiristocin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Mahmud Al-habbash babban alkalin alkalai na Falastinu, wanda yake gudanar da ziyarar aiki a halin yanzu a kasar ta Brazil.

Ya ce al’immar Brazil basa goyon bayan duk wani mataki na tauye hakkokin al’ummar falastinu, kamar yadda kuma ba su goyon bayan dauke ofishin jakadancin kasarsu zuwa Quds, domin hakan yunkuri ne na danne hakkin falastinawa da neman kwace Quds daga hannunsu.

Shi ma a nasa bangaren Mhamud Al-Habbash ya nuna farin cikinsa matuka dangane da matsayar da babban malamin addinin kirista na Brazil ya dauka, inda yake nuna goyon bayansa ga al’ummar Falastine, da kuma kin amincewa da duk wani zalunci a kansu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3864723

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Brazil ، Cardinal ، falastinawa ، alumma
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: