IQNA

Kabarin Maulana, Na Nuni Da Fasahar Musulmi A Tsawon Zamani

Jalaluddin Muhammad Balkhi wanda aka fi sani da Maulana, ya kasance fitaccen marubucin wakokin addini ta kasar Iran, . Ya tafi Sarmakand, daga can kuma ya wuce uwa Kuniya a kasar Turkiya ta yanzu.

Baitocin wakar Maulana dai sun fi karfi a bangaren yabon Allah madaukakin sarki, da kuma fito hikimomi na ayoyin kur’ani da ke magana kan kadaita ubangiji.

Bayan kwashe lokaci yana wannan gagarumin aiki, a shekara ta 1273 ya rasu a garin Kuniya yana dan shekaru 59 a duniya.

Bayan mutuwar Maulana, Tabrizli Badruddin Memar, da taimakon matar Sulaiman Parvaneh, Amir Saljuk da kuma dan Maulana suka gina makabartarsa, inda aka yi amfani da fasaha ta rubutun musulunci, ta hanyar sarrafa wasu kayan karau da kuma ababe na adon gini, inda aka rubu “Bismillah” da kuma “Ayatol Korsiy” da kaloli masu daukar hankali da natsar da zuciyar mai kallo.