IQNA

14:00 - January 08, 2020
Lambar Labari: 3484396
Tashar Fox News ta bayyana cewa, harin martanin da Iran ta kai wa sojojin Amurka babbar jarabawa ce ga Trump.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, daga tashar Alalam, tashar Fox News ta bayyana harin ramuwar gayya da sojojin Iran suka kai wa sojojin Amurka alardin Anbar na Iraki da cewa babbar jarabawa ce ga Donald Trump, kuma tana da wahalar ci.

Jaridar ta ce Trump dai ya zo kan shugabancin Amurka da taken kawo karshen duk wani yaki da Amurka take yi a duniya, amma kuma a halin yanzu ga inda ya kai kasar ta Amurka, kuma wannan ita ce shekarar da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka.

Abin tuni dai shi ne, a tsakar daren jiya ne dakarun IRGC na Iran suka yi lugudan wuta da makamai masu linzami a kan sansanonin sojin Amurka a kasar Iraki, domin daukar fansakan Kasim Sulaimani.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870224

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: