IQNA

21:16 - January 14, 2020
Lambar Labari: 3484412
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taron karawa juna sani a kan masallatan London.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a ranar 24 ga wannan wata na Janairu za a gudanar da zaman taron karawa juna sani kan masallatan London.

A yayin zaman taron za a amsa tambayoyi dangane da wasu lamurra da suka shafi addinin muslucni da suke shigewa wasu kai, musamman ma wadanda ba musulmi ba.

A wannan taro Shadah Rahman daga masallacin Cambridge, da kuma Kamran Sharzad daga cibiyar musulmi ta Bahu Trust, za su gabatar da jawai a wurin.

Masallacin Cambridge dai shi en masallaci mafi girma a kasar Birtaniya, wanda aka bude a  garin Cambriedge da ke tazarar kilo mita 80 daga birnin London, kuma yana daga cikin gine-gine guda 10 da suka dauki hankali a kasar a cikin 2019 da muke ciki.

Wanann masallaci yana da wurin salal wanda ke daukar dubban mutane a ciki da wajen masallacin, kamar yadda yake da wurare na karatu da alwala da kuma marakanta da wuraren nazari.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871530

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، nazari ، makaranta ، wurare
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: