IQNA

22:00 - January 16, 2020
Lambar Labari: 3484421
Magoya bayan Harkar Musulunci a Najeriya sun nuna rashin amincewa da ci gaba da tsare Sheikh Zakzaky a gidan kaso.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a cikin wani bayani da magoya bayan harkar suka fitar sun bayyana cewa, ci gaba da tsare sheikh Ibrahim Zakzaky a gidan kason Kaduan ya sabawa ka’ida.

A cikin bayanin wanda shugaban dandalin watsa labarai na harkar muslunci Ibrahim Musa ya fitar ya bayyana cewa, tun a cikin watan Disamban 2016 ne kotun tarayya ta bukaci a saki sheikh Zakzaky, da mai dakinsa, amma har yanzu ab a aiwatar da wannan umarni na kotu ba, wanda hakan ya sabawa doka ta kasa.

Baya ga haka kuma bayanin ya ce, bisa la’akari da yanayin malamin yake cikia  inda ake tsare da shi a halin yanzu, ya zama wajibi a dauki matakin kula da lafiyarsa yadda ya kamata, domin baya samun kulawar da yake bukata.

Daga karshe bayain ya kirayi kungiyoyin farar hula das u taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen batun tsare sheikh Zakzaky a Najeriya.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3871956

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: