IQNA

18:44 - January 17, 2020
Lambar Labari: 3484424
Gwamnatin kasar Birtaniya ta saka bangaren siyasa na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ministan harkokin cikin cikin gida na kasar Birtaniya Sajid Khan ya bayyana cewa, daga yanzu dukkanin bangarori na soji da kuma na siyasa na kungiyar Hizbullah, na a matsayin ‘yan ta’adda ne a wurin gwamnatin Birtaniya.

Ya cea  halin yanzu duk wasu bankuna da suke yin mu’amala da bangaren siyasa na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a Birtaniya dole ne su dakatar, domin yin hakan yana  a matsayin laifi ne a hukumancea  kasar.

Kamar yadda kuma ya ce duk wasu asusun ajiya na wasu mutane da suke da alaka da kungiyar za a rufe su tare da rike kudadensu.

Tun a  lokutan baya dai kasar Birtaniya ta saka bangaren soji na Hizbullah a cikin ‘yan ta’adda, duk da cewa babu wani dalili da gwamnatin Birtaniya ta gabatar kan wani aikin ta’addanci da kungiyar ta aikata a kasar.

Wannan mataki dai yana zuwa ‘yan sa’oi bayan gwamnatin Amurka ta sanar da daukar irin wannan matakin a kan kungiyar, inda gwamnatin ta Birtaniya take  yin aknzagi da amshin shata ga matakin na gwamnatin Amurka.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872233

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: