IQNA

20:45 - January 23, 2020
Lambar Labari: 3484443
Mataimakin shugaban kasar Iraki kan harkokin siyasa ya yi murabus daga kan aikinsa bayana ganawar shugaban na Iraki da Trump.

Kamfanin dillancin labaran IQNA daga Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, Ahmad Yasiri, Babban mataimakin shugaban kasar Iraki kan harkokin siyasa ya yi murabus daga kan aikinsa, domin nuna rashin amincewarsa da ganawar da ta gudana tsakanin Barham Salih da Trump a gefen taron Davos a kasar Swizerland.

A yammacin jiya ne dai shugaban na Iraki ya gana da shugaban Amurka,inda suka tattauna kan batutuwa na diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Abu Ali Alaskari daga kungiyar Hizbullah Iraki ya bayyana cewa, suna yin kakkausar suka dangane da ganawar da ta gudana tsakanin Bahm Salih da Trump, inda suke ganin hakan a matsayin rashin mutunta jinan Irakawa da Trump ya shekar a cikin kasarsu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3873645

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، Barham Salih ، Trump ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: