IQNA

Iran Ta Yi Tir Da Cin Zarafin ‘Yan Kasarta A Kasar Amurka

23:52 - January 26, 2020
Lambar Labari: 3484451
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi kakakusar suka kan cin zarafin Iraniyawa a filayen jiragen Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a zanatawarsa da manema labarai a birnin Tehran Abbas Musawi  ya bayyana cewa, irin matakan da jami’an tsaro suke dauka kan ‘yan kasar Iran a kasar Amurka, hakan ya yi hannun riga da dukkanin ka’idoji da dokoki na kasa.

Musawi ya ce baya ga haka kuma, hakan cin zarafin bil adama ne, domin kuwa dukkanin mutanen da ake cin zarafinsu ba su aikata wani laifi da ya saba wa wata doka a cikin kasar Amurka ba.

A kan haka ya ce yana kira ga mahukuntan Amurka da su gaggauta kawo karshen irin wannan dabi’a wadda ta saba wa ‘yan adamtaka.

Haka nan kuma ya bayyana cewa za su bi matakai na gaba domin bin kadun lamarin ‘yan kasar ta Iran da aka ci zarafinsu a kasar Amurka ta hanyoyi na doka.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3874035

 

 

 

captcha