IQNA

23:05 - January 27, 2020
Lambar Labari: 3484455
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Taliban ta sanar da harbon jirgin Amurka a cikin kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ya bayar da rahoton cewa, jirgin yana dauke da mutane 83 wanda ake sa ran sun rasa rayukansu.

Haka nan kuma rahotanni sun yi nuni da cewa a cikin jirgin akwai jami’an Amurka, duk kuwa da cewa Amurka ba ta ce komai kan batun ba, amma dai ta sanar da cewa ana gudanar da bincike.

Sai dai tuni a nata bangaren kungiyar taliban mai da'awar jihadi ta dauki alhakin harbo jirgin, lamarin da har yanzu mahukuntan Afghanistan ba su tabbatar da shi ba.

Wannan dai shi ne karon farko da ake harbo wani babban jirgi da ke dake daukar jama'a masu yawa a cikin kasar Afghansitan tun bayan da Amurka ta mamaye kasar shekaru 19 da suka gabata.

 

https://iqna.ir/fa/news/3874679

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Afghanistan ، lamarin ، jirgi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: