IQNA

Kiran Zanga-Zangar Falastinawa Domin Yin watsi Da Yarjejeniyar Karni

13:29 - January 29, 2020
Lambar Labari: 3484462
Bangarori daban-daban na falastinawa sun yi kira zuwa ga jerin gwano domin yin watsi da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, Kungiyoyin Falastinawa na gwagwarmaya da na siyasa da masu fafutuka duk sun yi kira ga Palasdinawa da su fito zanga-zangar yin allawadai da shirin Trump na yerjejeniyar karni wacce take nufin kwace wa Palasdinawa kasarsu.

A daren jiya Talata ce, daukacin kungiyoyin falastinawa suka yi wannan kiran ga dukkan magoya bayansu a duk inda suke a cikin falasdinu da su fara gudanar da zanga-zanga daga daren na jiya, domin nuna rashin amincewarsu da abin da ake kira yerjejeniyar karni.

Wasif Abu Yusuf jigo ne a kungiyar Fatah, ya bayyana cewa suna nan a kan matsayinsu na kin amincewa da shirin na Trump, inda ya bayyana hakan da cewa yunkuri ne na neman kawo karshen batun kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Hamas da sauran kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza, sun fitar da bayanai da ke tabbatar da cewa suna goyon bayan matsayar da gwamnatin Falastinawa ta dauka, na yin watsi da shirin na Trump.

Har’ila yau tun daren jiya ne, dubban falastinawa a yankunan zirin gaza da gabar yamma da kogin Jordan, suka fara gudanar da zanga-zangar yin tir da wannan shiri, tare da kona hotunan Trump da Netanyahu da kuma yarima mai jiran gadon saraunta na kasar Saudiyya gami da yariman hadaddiyar daular larabawa, don nuna fushinsu da shirin.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875006

captcha