IQNA

23:55 - January 31, 2020
Lambar Labari: 3484467
Baitul malin kasar Amurka ya sanar da kakaba takunkumai a kan shugaban hukumar makamashin nukiliya ta ran.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, takunkuman Amurka a kan dukaknin bangarorin hukumar makamshin nukiliya ta Iran da kuam shugaban hukumar Ali Akbar Salihi sun fara aiki.

A daya bangaren Jami’in Amurka kan batutuwa da suka shafi Iran ya bayyana cewa, kasarsa ta kara wa’adin daga kafa domin yin mu’amala da hukumar makamashin nukiliya ta Iran har zuwa kwanaki 60 a nan gaba.

Kafin wannan lokacin dai Amurka ta sanar ad kakaba takunkumai a kan manyan jami’an gwamnatin Iran, bisa hujjar cewa yin hakan ne zai sanya Iran ta mika wuya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875293

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: