IQNA

Saudiyya Ta Yaba Wa Trump Kan Abin Da Ta Kira Yunkurinsa Na Samar da Zaman Lafiya

23:59 - February 04, 2020
Lambar Labari: 3484486
Gwamnatin Saudiyya ta jinjina wa Donald Trump kan abin da ta kira kokarin da yake na wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin Saudiyya ta yaba  wa Donald Trump kan abin da ta kira kokarin da yake yi na wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, musamman tsakanin falastinawa da Israila.

Wannan sanarwa ta zoa  zaman da majalisar ministocin kasar ta Saudiyya ta gudanar a ranar Litinin da ta gabata ce.

Bayanin zaman ya ce, gwamnatin Saudiyya tana jinjina wa shugaba Trump kan namijin kokarin da yake na kawo zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya, tare da bayyana hakan a matsayin aikin yabawa.

Wannan dai na zuwa nea  daidai lokacin al'ummomin larabawa da musulmi suke ci gaba da yin watsi da shirin na Trump ne, wanda ya gabatar da sunan shirin zaman lafiya tsakanin falastinawa da Isra'ila, ko kuma yarjejeniyar karni.

A cikin shirin na Trump an haramta wa falastinawa kafa kasarsu mai cin gishin kanta, sai dai su ci gaba da zama karkashin danniya da mulkin yahudawa, kamar yadda kuma shirin na Trump ya mika birnin Quds ga Isra'ila da ma wasu yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876615

captcha