IQNA

23:35 - February 06, 2020
Lambar Labari: 3484491
Kungiyar Amnesty International ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira hukunta mutane da ake a yi Saudiyya saboda ra’ayinu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa,a cikin wani bayani da kungiyar Amnesty ta fitar a yau Alhamis, ta bayyana cewa abin takaici ne yadda ake kame mutane a daure su ko a kashe su saboda dalilai na siyasa, ko na banbancin akida ko ra’ayinsu a kan yadda ake tafiyar lamarin kasa da ake yi a Saudiyya.

Hiba Murayif bababr darakta ta Amnesty International a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika ya bayyana cewa, daga shekara ta 2011 zuwa 2019, an yanke wa mutane 95 hukunci a Saudiyya, da suka hada da ‘yan jarida, malaman addini, da ‘yan kungiyoyin farar hula masu fafutukar kare hakkokin jama’a, wanda wasunsu tuni an riga an fille musu kawuna.

Ta ce daga shekara ta 2008 ne aka kafa wata kotun hukunta laifukan ta’addanci, kuma daga lokacin lokacin dukkanin mutanen da kotun ta yankewa hukunci babu wani dan ta’adda, sai dai wadanda suke fadar albarkacin bakinsu, ko kuma saboda dalilai na banbancin mazhaba, ko kuma suna bayyana ra’ayinsu wanda hakan ba ya yi wa masu mulki dadi.

Kungiyar ta ce tana kira da a aggauta sakin dukkanin mutane ad ake tsare da su saboda ra;ayinsu na siyasa ko kuma banbancin akida.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876430

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Afirka ، Saudiyya ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: