IQNA

23:37 - February 06, 2020
Lambar Labari: 3484492
Isra’ila ta kai hare-hare da makamai masu linzami a kusa da birnin Damascus na Syra, amma makaman kariya na Syria sun kakkabo makaman na Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, gwamnatin Siriya ta sanar da murkushe wani harin makamai masu linzami da mahukuntan yahudawa mamaya na Isra’ila suka kaddamar a cikin daren jiya a wasu sassan kasar.

Kamfanin dilancin labaren kasar, ya rawaito cewa makamman garkuwa kan hare haren sama sun murkushe wasu jerin hare haren makiya a kusa da Damascus babban birnin kasar.

Hare haren an kai su ne kan yankunan al-Kiswah da Marj al-Sultane da Jisr Bagdad, inda wuta kama a daya daga cikin sansanonin sojin gwamnatin Siriyar.

Wannan dai ba shi karon farko ba da Isra’ila da ke kai ire iren wadannan hare hare a Siriya ba, tun bayan barkewar rikicin kasar a cikin shekara ta dubu biyu da sha daya.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876975

Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، syria ، Damascus ، Hari
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: