IQNA

23:54 - February 07, 2020
Lambar Labari: 3484494
Daruruwan jami’an tsaron yahudawan sun afkawa musulmi a lokacin gudanar da sallar asuba a yau Juma’a.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, jami’an tsaron yahudawan sun afkawa musulmi a lokacin gudanar da sallar asuba a yau Juma’a tare da yin artabu da su, amma duk da haka dubban musulmi sun damar yin salla.

A cikin yan makonnin dai yahudawan Israila suna daukar matakan hana musulmi yin sallar asuba  acikin masallacin Quds, musamman ma ganin cewa a halin yanzu duban musulmi ne suke dukkanin salloli a  cikin masallacin mai alfarma, musamman sallar asubahi.

Mutane da dama ne daga cikin masallatan suka samu raunuka, sakamakon dukarsu da kulake da ‘yan sandan yahudawa suka yi, domin hana su shiga cikin masallacin quds domin kada su yi salla.

Haka nan kuma yahudawan sun yi awon gaba da Aida Saidawi, daya daga cikin masu gadin masallacin quds mai alfarma.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877115

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، asuba ، salloli ، kulake ، yahudawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: