Kamfanin dillancin labaran IQNA, kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, a cikin hudubar sallar Juma’a ta yau a na karanta sakon Ayatollaj Sistani.
Bayanin ya ce, Ayatollah Sistani ya jaddada a kan batutuwa biyu, na daya daga cikinsu shi ne jama’a masu neman gyara da su yi amfani da hanyoyi na lumana, ba na tashin hankali ba.
Haka nan kuma ya kirayi jami’an tsaro da su kare masu zanga-zangar lumana domin neman a yi gyara a cikin harkokin tafiyar mulkin kasar.
Baya ga haka kuma ya kirayi gwamnati da ta gaggauta aiwatar da sauye-sauye domin al’ummar kasar ta gani a kasa, kamar yadda ya yi kira da a gudanar da zaben gaggawa.
https://iqna.ir/fa/news/3877123