IQNA

23:51 - February 09, 2020
Lambar Labari: 3484501
Mamba a kwamitin tsaro an majalisar dokokin kasar Iraki ya bayyana cewa, sojojin Amurka sun fara ficewa daga kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin Baghdad Al-yaum ya bayar da rahoton cewa, mamba a kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar Iraki Ali Ghanimi ya bayyana cewa, Amurka ta fara janye sojojinta daga Iraki.

Ya ce a halin yanzu Amurka tana fitar da sojojinta daga sansanoni 15 da ta jibge sojojinta a Iraki.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, sansanonin soji biyu ne kawai sojojin Amurka za su yi saura  a cikinsu, daya yana arewacin kasar ne a lardin Arbil, sai kuma guda a yankin Ainul Assad.

Dan majalisar ya ce duk da haaakaaa da dama cikin ‘yan majalisar dokokin Iraki da ma mutane da dama daga cikin al’ummar kasar suna ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin Iraki, kan ta gaggauta daukar matakan ficewar sojojin Amurka baki daya daga kasar.

A kwanakin baya dai kakakin maaikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya bayyana cewa, Amurka ba ta niyyar fitar da sojojinta daga kasar Iraki.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877732

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sojojin Amurka ، ficewa ، daga ، Iraki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: