IQNA

23:54 - February 09, 2020
Lambar Labari: 3484502
An gabatar da wani shiri na musamman kan juyin juya halin usulunci na kasar Iran a gidan radiyon kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, an gabatar da wani shiri an musamamn kan juyin juya halin muslunci a kasar rana  gidan radiyon kasar Uganda.

Karamin jakadan Iran a Uganda Muhammad Ridha Qazalsufli da kuma wani masani kan harkokin addini na kasar Isa Chgungo, suna daga cikin wadanda suka yi bayani a cikin shirin.

Isa Chigungo ya bayyana cewa, juyin na Iran yana daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a cikin wanann karni, wanda kuma ya wakana ne bisa jagoranci an hikima na marigayi Imam Khomeni, duk da irin matakan da mayan kasashen duniya suka dauka domin murushe juyin.

Shi ma a nasa bangaren karamin jakada na kasar ta Iran a Uganda ya yi Karin bayani kan muhimman lamurran da suka wakana a lokacin juyin, har zuwa lokacin samun nasararsa.

Ya kuma bayyana cewa, daya daga muhimman lamurra da suke a gaba a siyasar kasarsa shi ne bunkasa alaka da kasashen nahiyar Afrika.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877502

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: