IQNA

20:54 - February 13, 2020
Lambar Labari: 3484518
Gwamnatin kasar Japan ta bayar da taimakon kudade hard ala miliyan 32 ga al’ummar falastinu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin Japan ta sanar da cewa, wadannan kuadde suna daga cikin irin taimakon da ta saba yi na jin kan dan adam ga alummar falastinu.

Cibiyar taimaka ma falastinawa da ke karkashin majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gudanar da ayyuka na taimaka ma mata da kananan yara, kamar yadda kuma za a yi amfani da wani bangaren kudade wajen gudanar da wasu ayyka a bangaren kiwon lafiya tare da hadin gwiwa da red cross.

 

https://iqna.ir/fa/news/3878538

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Japan ، taimako ، falastinawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: