Kamfanin dillancin labaran Associated press ya bayar da rahoton cewa, mahukuntan Amurka sun tabbatar da bullar cutar ta corona a cikin kasar.
Ita ma a nata bangaren tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, ya zuwa yanzu akalla mutane 60 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a cikin kasar Amurka.
A cikin makon nan wasu daga cikin ‘yan majalisar dattijan kasar Amurka da suka musamman daga jam’iyyar Democrat, sun caccaki gwamnatin kasar kan jan kafar da take wajen dauakar matakan kariya a kan cutar.
A nasa bangaren shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya mayar da martani a cikin izgili, yana mai cewa wannan cutar ba za ta yi wani tasiri a cikin Amurka ba, domin kuwa mutum biyu ne kawai suka kamu da ita, kuma ana kula da su.