IQNA

Masallacin "Alfar" wanda a cikin harshen kasar ake kira da "saman koto bali" wato jan masallaci, yana a garin Colombo fadar mulkin kasar. Dadadden massalaci ne wanda ake lissafa shi cikin muhimamn wurare na tarihi, an kammala gininsa a cikin 1909.