IQNA

23:53 - March 04, 2020
Lambar Labari: 3484584
Tehran (IQNA) Su’ad Abdulkadir tsohuwa ce mai shekaru 77 da ta rubuta cikakken kur’ani a Masar.

Shafin yada labarai na sba۷egypt.com ya bayar rahoton cewa, Su’ad Abdulkadir tsohuwa ce mai shekaru 77 daga yankin Iskandariyya na kasar Masar, wadda da ta rubuta cikakken kwafin kur’ani mai tsarki.

Wannan mata tana ware sa'oi 7 zuwa 8 daga lokacin da ta yi sallar asuba, domin rubutun kur'ani mai tsarki, har zuwa lokacin da ta kammala wanda ya dauke ta shekaru biyu.

Daya daga cikin jikokinta ne dai ya dauki hotunanta kuma ya watsa  a shafukan yanar gizo, inda ya bayyana cewa kakarsa ba ta yi karatu ba, amma Allah ya yi mata baiwar ta karatun kur'ani mai tsarki.

 

 

3882957

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Masar ، rahoto ، rubuta ، tsohuwa ، kwafin kur’ani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: