IQNA

Pakistan Ta Jinjina Wa Jagoran Juyi Na Iran Kan Kare Musulmi Na India Da Ya Yi

23:46 - March 05, 2020
Lambar Labari: 3484589
Tehran (IQNA) Ofishin shugaban kasar Pakistan ya aike da sakon jinjina ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, kan kare al’ummar musulmi na kasar India da ya yi.

Bayanin da shafin twitter na shugaban kasar Pakistan ya watsa, ya yaba matuka da irin matakin da matakin da jagora Imam Khamenei ya dauka na nuna damuwa kan halin da musulmin India suke ciki, tare da kiran mahukuntan kasar da su gaggauata daukar matakin dakatar da kisan musulmi.

Bayanin ofishin shugaban kasar Pakistan ya ce, abin da yake faruwa a kasar India kan musulmi, yana nuni ne da abin da ya faru na kisan kiyashin da ‘yan NAZY suka yi a Jamus, da kuma kisan kiyashi kan musulmi da aka yi a Myanmar.

A yau ne Jagoran juyin juya hali na kasar Iran ya isar da sakonsa ga mahukuntan kasar India, kan wajabcin taka burki ga ‘yan addinin Hindu masu tsatsauran ra’ayi, wadanda suke yin kisan kiyashi kan musulmin kasar.

3883454

 

 

captcha