IQNA

23:01 - March 09, 2020
Lambar Labari: 3484603
Tehran (IQNA) mahukunta a kasar Saudiyya sun sanar da bayar da hutu a makarantun kur’ani na kasar saboda corona.

Shafin yada labarai na Almisriyun ya bayar da rahoton cewa, Abdultif Al Sheikh minsta mai kula da harkokin addini a kasar saudiyya ya sanar da cewa, saboda tsoron yaduwar cutar corona, an bayar da hutu a makarantun kur’ani na kasar.

Ya ce tun kafin wannan lokacin suna daukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an kaucewa yaduwar cutar a tsakanin jama’a, wanda hakan ya hada taruka na mutane da yawa  awuri guda.

Ya ce tsarin karatu na halka da  ake yi a  kasar inda mutane da dama suke taruwa a wuri guda yana da hadari, kuma za a iya kamuwa da cutar matukar aka yi rashin sa’a wani mai dauke da ita ya shiga wurin.

Yanzu haka dai cutar corona ta kama mutane kimanin dubu 109 a fadin duniya, inda ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da 3,800 daga cikinsu.

3883979

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: