IQNA

WHO Ta Sanar Da Corona A Matsayin Cuta Ta Duniya Baki Daya

23:58 - March 12, 2020
Lambar Labari: 3484616
Tehran (IQNA) Hukumar lafiya ta duniya  ta bada sanarwa kan cewa cutar coronavirus mai shafar numfashi ta zama mummunar annoba a duniya.

Majiyoyin hukumar sun ce shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar damuwarsa akan yadda cutar take saurin yaduwa a duniya.

Ghebreyesus ya ce yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a wajen China, ya ninka shi har sau sha uku a cikin makwanni biyu da suka gabata, kuma tabas a cikin makwanni masu zuwa adadin wadanda zasu kamu da da cutar za su karu kamar yadda wadanda za ta kashe ma za su karu.

Tedros ya ce dole ne kasashen duniya su tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace don yakar cutar ta hanyar fadakar da jama’arsu kan hatsarin cutar da kuma hanyoyin kare kai daga cutar.

A hannu guda kuma hukumar ta ce Iran, wacce ke cikin kasashen wadanda cutar ta fi kisa a cikinsu, tana iya kokarinta, saidai ta na fama da matsananciyar matsalar kayakin aiki.

Kawo ya yanzu dai, adadin mutanen da cutar ta kashe a fadin duniya ya haura dubu hudu.

 

3884850

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha