IQNA

8:37 - March 14, 2020
Lambar Labari: 3484620
Tehran (IQNA) magatardan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana yaki da cutar corona a matsayin aiki ne na ‘yan adamtaka zalla da ke al'umma.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya wanda kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar Lebanon suka watsa kai tsaye, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah, ya yi ishara da wajabcin hada karfi tsakanin al’ummomi domin yaki da cutar corona a duniya baki daya.

Ya ce nauyi na farko ya rataya ne kan hukumomi da cibiyoyin kiwon lafiya na duniya da kuma na daidaikun kasashe, kamar yadda kuma masu hannu da shuni za su iya taimaka wa da duk abin za su iya domin gudanar da wannan aiki na ‘yan adamtaka.

Haka nan kuma dangane da sauran jama’a kuwa, Sayyid nasrullah ya bayyana cewa, mataki na farko na fuskantar lamarin shi ne dogaro ga Allah, da kuma kaskantar da kai a agare shi da rokonsa kariya, sannan kuma a kiyaye dukkanin abubuwan da masana da cibiyoyin kiwon lafya suke fada dangane da lamarin da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Nayyid Nasrullah ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald a matsayin babban makaryaci, dangane da yadda ya yi ta shirga wa duniya karya kan batun cutar ta corona, da kuma yadda yake nuna cewa lamarin ba zai taba shafar Amurka da Burtaniya ba sakamakon matakan da suka dauka kan batun.

Haka nan kuma a lokacin da ya koma kan hare-haren da Amurka ta kaddamar jiya Juma’a  akan sansanonin sojin kasar Iraki kuwa, ya bayyana hakan da cewa abin Allawadai dai, tare da tabbatar da cewa Amurka ce take kara kusanto da lokacin ficewar daga kasar Iraki da kanta ta hanyar aikata irin wadannan laifukan yaki.

 

3885079

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: