IQNA

23:55 - March 16, 2020
Lambar Labari: 3484629
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Sudan ta amincewa Isra’ila da ta yi amfani da sararin samaniyarta domin wucewar jiragenta.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Sudan ta cimma yarjejeniya tare da babban kamfanin jirage a yankin Latin Amurka na LATAM, kan yin amfani da sararin samaniyar Sudan domin zuwa Isra’ila.

Bisa ga wannan yarjejeniya da aka cimmawa, tsawon tafiyar da jirage suke yi daga latin Amurka zuwa Tel aviv, ko kuma akasin hakan, zai ragu matuka.

Tun a kwanakin baya ne firai ministan Isra’ilaBenjamin Netanyahu tare da shugaban majalisar shugabancin kasar Sudan suka cimma matsaya kan kyautata alaka tsakanin Sudan da kuma Isra’ila, a wata ganawa da suka yi a kasar Uganda.

LATAM shi ne kamfanin jirage mafi girma  ayankin latin Amurka baki daya, wanda yake da jirage da suke safara da yawansu ya haura 300, da suke zirga-zirga a kasashen duniya.

3885692

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Sudan ، kyautata alaka ، tsakanin ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: