IQNA

22:19 - March 19, 2020
Lambar Labari: 3484636
Tehran (IQNA) shugaban Iran ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekarar Norouz ga shugabannin kasashen Afghanistan, Pakistan, Azarbaijan, Turkmenistan, Armania, Tajikistan, Turkiya, Qazakistan, Kirgistan, Iraki, da kuma Uzbakestan.

Shafin yada labarai na shugaban kasar Iran ya nakalto cewa, a yau shugaba Rauhani ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekarar hijira shamsiyya ta 1399 ga takwarorinsa na yankunan da ake magana da harshen farisanci ne kamar yadda ya saba yi a kowace shekara, domin taya su murnar shiga shekarar da kuma yi musu fatan alhairi tare da al’ummominsu.

A cikin sakon nasa shugaba Rauhani ya bayyana cewa, wannan shekara ta zo da ibtila’i daga ubangiji, inda cutar corona ta bulla a kasashen duniya, kuma Iran tana daga cikin kasashen da cutar ta fi yi wa illa.

Ya e abu ne ya zama wajibi a kan dukkanin al’ummomin kasashe su hada karfi da karfe domin yaki da wannan cuta, wadda take yin barazana ga rayuwar ‘yan adam baki daya a halin yanzu.

Daga karshe ya yi fatan samun nasara wajen shawo kan wanann cuta a duniya baki daya, kamar yadda kuma ya yi fatan alhairi da samun zaman lafiya da bunkasar arziki ga dukkanin al’ummomin kasashen musulmi baki daya.

3886556

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Shugaba Rauhani ، ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: