IQNA

23:55 - March 23, 2020
Lambar Labari: 3484649
Tehran (IQNA) Jaridar Isra’ila ta bayar da rahoton cewa babbar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta sanar da dakatar da bincike kan laifukan Isra’ila a yankun Falastinawa.

Jaridar Isra’ila ta Yisrael Hayom ta bayar da rahoton cewa, sakamakon yaduwar cutar corona, babbar mai shigar da kara a gaban kotun manyan laifuka ta duniya Fatou Bensouda ta sanar da dage bincike kan laifukan yaki na Isra’ila a kan Falastinawa a gabar yamma da kogin Jordan.

Jaridar ta ce wannan shi kadai babban amfanin cutar corona ga Isra’ila.

A karshen wannan wata na Maris dai ake zaton cewa kotun manyan laifuka ta duniya za ta kammala bincikenta da kuma sanar da hukuncinta kan zargin Isra’ila da tafka laifukan yaki kan Falastinawa mazauna yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

A cikin wani sako da ta aikewa kotun manyan laiuka ta duniya dake birnin Hague, Fatou Bensouda ta bayyana cewa, ba za ta iya kammala binciken da take yi zuwa karshen wannan wata kan laifukan yakin Isra’ila ba, saboda matsala corona.

Bensouda ta ce aikin zai dauki lokaci daga har zuwa wata mai kamawa.

 

 

3887099

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: