IQNA

23:46 - March 31, 2020
Lambar Labari: 3484670
Tehran (IQNA) an rufe makarantun kur’ani mai tsarki a fadin kasar Somalia domin hana yaduwar cutar corona.

Shafin yada labarai na Somali Aljadid ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Somaia ta sanar da cewa, rufe makarantun zai ci gaba har zuwa tsawon makonni biyu masu zuwa.

Bayanin ya ce manufar hakan dai ita ce dakile yaduwar cutar corona a tsakanin jama’a.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Somalia ta bayar da umanin rufe makarantun book da suka hada da jami’oi da saurantu na firamare da sakandare.

Ya zuwa daren jiya an sanar da cewa mutane dubu 735 suka kamu da cutar ta covid-19 a duniya, dubu 34 da 847sun rasa rayukansu, dubu 156 da 142 sun samu lafiya.

3888319

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Somalia ، makarantan kur’ani ، a fadin kasar ، rufe ، saboda ، cutar corona
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: