IQNA

Martanin Falastinawa Kan Harin Da Isra’ila Ta Kai Syria A Jiya

23:52 - April 01, 2020
Lambar Labari: 3484674
Tehran (IQNA) kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sun ce ci gaba da kai wa Syria hari da Isra’ila ke yi abin Allawadai ne.

Shafin yada labarai na falastinawa ya habarta cewa, mai Magana da yawun kungiyar gwagwarmayar musuluncin ta Hamas, Hazim Qassim, ya fadawa kamfanin dillancin labarun; “Iran” na Iran cewa; Ya zama wajibi ga al’umma da ta hada karfi da karfe wuri daya domin fuksantar wuce gona da irin ‘yan sahayoniya da taka musu birki.

A nata gefen, kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta “Popular Front” ta yi tir a harin na ‘yan sahayoniya wanda ya yi sanadin shahadar Birgediya janar Khalaf Jasim, tare da cewa; ci gaba da wuce gona da irin na ‘yan sahayoniya akan kasar Syria.

Kungiyar ta nuna cikakken goyon bayanta ga Syria tare da yin kira ga dukkanin al’ummar larabawa da su yunkura domin taimakawa Syria a fadan da take yi da ‘yan sahayoniya.

3888554

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha